Raddi ga Ben Shapiro akan Yiwa Falasdinawa Kisan Kare Dangi- Cif Femi Fani Kayode, Sadaukin Shinkafi

"Gaza ke, bakar mace, tarin shara, Gaza ke, karuwa, yar karuwa kamar uwarki itama karuwa inji Lior Narkis.

Wudannan sune irin kalamanda mawakin israila Lior Narkis ya ringa rerawa a tsakiyar dubun dubatan yahudawa da sukayi dandazo a sansanin sojojin Israila a daidai lokacinda Israilan ke yiwa zirin Gaza ruwan bama bamai, kwanaki kadan kafin kasar ta Israila ta tura dakarunta na kasa zuwa zirin Gaza. 

Wannan ne dalilinda ya tursasani na tambayi Bayahuden kasar Amurka kuma marubuci wanda ya kasance dan gani kashenin goyon bayan kisan kiyashinda kasar Israila ke yiwa Falasdinawa. Ben Shapiro ya kasance mutum mai dinbim magoya baya, kuma mai fada aji a fadin duniya. 

Shin Mr. Shapiro irin wannan babatu da kin gaskiya da kuma yada labaran kanzon kurege akan kasar Israila ne kukeson kowa da kowa a duk fadin duniya ya aminta dasu ba tareda yin binciken gaskiyar abunda ke faruwa ba?

Kamar yadda wani masani yayi tambaya shin meyasa wannan mawakin na kasar Israila ke samun damar zagaye da kuma shanya garinsa a sansani dabban dabban na sojojin kasar Israila a lokacinda ya kamata ace mahukunta sun bincikeshi akan yada kalaman kin jinin larabawa da kuma laifukan yaki da ka iya kai ga kisan kiyashi ga fararen hula ?

Ansar tambayoyin nan ba abu bane mai wahala, saboda hakan na nuni ne da irin akidar tsana da rashin kaunar da yahudawa zayonawa (Zionist) keyiwa larabawa ba kawai larabawan ba a,a akan duk wani mutum mai launin fata.

Tabbas kalar wakokinsa da irin tunaninsa abun kyama ne, wanda addinina na kiristanci ya umurceni da in kyamace su da duk wani mai irin wannan tunanin ko akidar da duk karfina, jinina da jijiyata.

Ina matukar mamakinka Mr. Shapiro a matsayinka na babban mai kare muradi da kudurin kisan kiyashinda Isarila keyiwa mata da kananan yaran Falasdinawa idan har kanada wani abun cewa ko kanada kwarin guiwar fitowa ka kare irin wannan matakin, ko kuma kayi Allah waddai da kisan kiyashi, kisan gilla dama keta hakkin dan Adam dake faruwa a Gaza. 

Abun bakin cikin shine idan mutum yayi la,akari da irin kalaman batanci, wariyar launin fata, tsantsar kiyayya da kuma rashin imaninda kake nunawa a rubuce rubucenka a jaridar Amurka mai suna " American Daily Wire" da kuma abunda kake yadawa a kafafen yada zumunta na manhajar X gaskiya banyi tsammanin zaka iya yin Allah wadai da irin wannan cin zarafin ba. 

Ina sake neman uzuri daga gareka Mr. Shapiro domin in kawo maka wata muhimmiyar gudun mawa daga bakin shugaban kasar Brasil, " President Lula Da Silva" inda yake cewa.

" Idan Hamas ta aikata ayukan ta,addanci, kasar Israila ma tana aikata ayukkan ta,addanci. Ban taba jin inda aka kira kananan yara ba a matsayin mayaka, yawan mata da kananan yaran Falasdinawa da suka mutu ba,a taba samun irin shi ba a tarihin yaki a duniya, Su (Israilawa) suna kashe mutane wudanda basuji ba basu gani ba."

Ina mai baka shawara da cewa ka saurari wudannan kalaman da kunnen basira ka kuma yi amfani dasu domin wannan itace fahimtar mafiyawanci mutanen duniya wayayyu masu hankali. 

Tsokacin a yanzu shine. 

Yakai Mr. Ben , ina baka wannan shawarar ne saboda wasu dalilai da suka sa nafi daukarka da muhimmanci fiye da sauran ire irenka saboda irin karfin halinka wajen tauye gaskiya, munafunci  da kuma kwarewarka wajen yaudara, da saura akalar tarihi da iya yada labaran kanzon kurege da yasa ka zamo mutum  mai matukar hatsari. 

Wato sassauta maka danayi ne yasa nace kai din kawai wani sabon Josef Goebbels ( Ministan jita jita na jamiyyar Hitla) samfurin Amurka amma idan akasaka ka a ma,auni ko mizani na hankali to kai manufarka ba wai ta tawaya ne kawai akan kasar Jamus ko Amurka ba ta shafi dukkan duniya ne. 

Aikinka shine ka kare karyarda bazata karu ba, ka rufe cin zarafinda bazai boyuba. 

Kana ci gaba da yaudarar milyoyin mutane a duk fadin duniya da karairayinka kana yada muradunka na zubarda jini, mulkin mallaka, da zalunci ta hanyar amfani da kafafen yada labarai da kuma kafafen sada zumunta ka mayarda gaskiya karya ka kuma mayarda karya gaskiya. 

Badon cewa zautattun mutane da yawa na karanta tatsuniyoyinka ba a fadin duniya suna kuma amfani dasu a matsayin gaskiya da sam bazan damu da in dauki alkalami da takarda in rubuta maka wannan doguwar wasikar ba. 

Kodayake irin rashin son gaskiyarka, tauye jawabi da kuma yada labarun karya akan al,ammurranda suka shafi kisan kiyashi da laifukan yakinda gwamnatin kasar Israila da kuma sojojinta ke aikatawa a zirin Gaza dama kasar Falasdin baki daya da kuma irin kiyayya da tsana da kake nunawa duk wani wanda bai goyi bayan labarin kanzon kuregenda kake yadawa ba ya isa ya zamo wani mihimmin dalili da zan baka ansa.  

Kafin in shiga bayani akan mummunar aika aikanda ke faruwa a zirin Gaza ina neman uzurinka domin nayi tsokaci akan irin halin wariyar launin fata da kuma tsantsar kiyayya da rashin son gaskiyarka. 

A 27 ga watan Satumba 2010 kayi rubutu kamar haka a shafinka na manhajar X:

" Israilawa nada ra,ayin ginegine, larabawa nada ra,ayin konawa da kuma zama a cikin bola, wannan ba abu bane mai wahala ".

Ina tambayarka shin wannan irin kalaman ba wariyar launin fata bane? Ba cin zarafin dan Adam, da kuma nuna tsantsar tsana da kiyayya bane?

Irin kalaman batancinda kake amfani dasu akan larabawa na tuna man da irin kalaman da turawan mulkin mallaka na kasar Afrika ta Kudu suka ringa yi akan bakaken fatar kasar wanda har takai suna cewa bakaken kasar basukai matsayin mutane ba, kaskantaccin bayi wudanda basuda asali ko wata gata. Wanda a kundin tsarin mulki na gwamnatin mulkin mallaka ta lokacin ta ce su ba komai bane face masu saran itace da kuma debo ruwa da zimmar kamantasu da wani labari a cikin littafin Bible wanda mabiya addinin kirista mukayi ammana dashi. 

Haka kuma kalamanka na tuna man da  kalaman wani mai yawon bincike binciken kasashe da nahiyoyi dan kabilar Dutch mai suna Jan Van Reebeck wanda dayane daga cikin turarwan farko da suka fara ziyartar kasar ta Afrika ta kudu, wanda saukarsa keda wuya ya kira yan uwan masu launin fata yan asalin Afrikan ta kudu da " Bakaken karnuka masu wari."

Maganar gaskiya itace mutane masu magana da tunani irin naka sune mutane mafi muni akan Nazi na kasar Jamus wudanda suka bautarda kakannin kakanninka da zimmar yimasu kisan kare dangi. 

Ko shakka babu ina zargin cewa an dauki cikinka, an kuma haifeka tareda renonka a irin wannan bolar dakake alakanta larabawa a zama a ciki. 

Zance akan Gaza. 

Zanso ka sake yiman uzuri domin zan fara ne da kalaman Mai Martaba Abdullah Abu Sawesh, wanda ya kasance jakadan kasar Israila a kasata Nigeriya. 

A wata sanarwa ta musamman daya fitar ga manema labaru a wannan satin yana cewa:

" Cikakken goyon baya da daurin gindin da kasar Israila ke samu daga kasashen yammacin duniya ne ya kara karfafawa da kuma kawo cigaban kisan kiyashi da kuma Nakba data fara a shekarun 1948. Ci gaba da yada jita jita da kuma goyon bayan masu mulkin mallaka da kafafen jaridun kasashen na turai ne yasa suka zamo da hannu dumu dumu a wannan kisan kiyashin.  A kwana na 40 da fara wannan mummunar kisan gillan, duk wani labari da ya fito daga kasar Falasdin gaba daya ko zirin Gaza a takaice ya kasance maras dadin ji. Abun bakin ciki bani da wani zabi face in fara da alkalumma marasa dadinji da suka hada da mutuwar Falasdinawa fararen hula dubu goma sha biyu (12,000) wudanda mafi yawancinsu matane da kananan yara. Daga ciki akwai mutane sama da dubu biyu da suka bata, har yanzu anajin nishi daga karkashi kasa data binne dubban mutane, kenan kawo yanzu akwai mutane dake yakin zama a raye da tarin kankare ya binne saboda tashin bama bamai da Israila ta harbi. Haka alkalumman mutanenda suka muta a bangaren gabar yamma na karuwa inda sama da Falasdinawa 186 suka jikkata haka 2'400 suka samu mummunan rauni. Haka kuma daruruwan mutane yanzu a haka suna rubewa a farfajiyar asibitin Al-Shifa, a kan tituna dabban dabban, babu wata hanya dama za,a samu a binne gawarwakin wudanda suka rigamu gidan gaskiya saboda ruwan bamabaman da Israila keyi. Fiye da yan jarida 750 daga gomman gidanjen jarida ne suka sa hannun a budaddiyar wasika inda sukayi Allah wadai da irin goyon bayanda gidajen jaridun Kasashen yamma ke bayarwa ga wannan kisan na kare dangi a zirin Gaza. Inda wasikar ke cewa gidajen yada labaran sun zamo wasu kafafe na goyon bayan zubarda jini, wariyar launin fata da kuma kisan kare danginda akeyiwa Falasdinawa. 

Shin akwai wanda zaiji irin wudannan kalaman ba tareda ya zubarda hawaye a boye ba ga Falasdinawa?

Shin hakan bayana nuni da cewa akwai wata manufa mabayyaniya ba, da zimmar yiwa Falasdinawa kisan kiyashi da kuma kawardasu daga bayan kasa?

Wannan ba zancen yaki da Hamas bane ko kuma Yunkurin kawarda yan ta,adda ba, wannan wani yunkuri ne na kashe dukkanin Falasdinawa maza,mata, yara kanana da zimmar kawardasu daga bayan kasa da kuma shafe duk wani tunaninsu. 

Wannan shine irin abinda tsofaffin turawan "Mahaukaciyar yamma" ( wild-west) sukayiwa Indiyawan daji asalin masu kasar Amurka, wannan shine abunda yahudawa zayoniyya keson maimaitawa a kasar Falasdin. 

Suna muradin su karyasu, su tarwatsasu, su kawar dasu su  sannan sauran tsirarunda suka rage su killacesu a sansani a Saharan  Sinai su ringa wulakantasu kamar bayi kaskantacci kuma mabarata. Wannan itace manufar Israila. 

Allah ya sawaqa ya kare wannan bazai taba faruwa ba.

Wannan shine abunda yahudawa zayoniyawa mahaukata, mayaudara yan handama da babakere irinku Mr. Ben ke fata, shine burinku domin samun damar mamayewa tareda sace kasar Falasdinu da zimmar samun riba, mulki, da sauran ma,adinaai dake zube birjik a kasar Falasdinu musamman zirin Gaza da kewaye. 

Kwanki kadan da suka gabata ka saka hoton wani rame wa mabiyanka milyan 6  a manhajar X. 

Kayi ikirarin cewa wannan ramen an sameshi ne a karkashin asibiti a zirin Gaza, inda kace wannan ramen ya bulla ne zuwa wasu ramuka na mayakan Hamas ta karkashin asibitin. 

Amma kamar kullum ka kasa kawo wata kwakkwarar hujja dake gaskata irin wannan ikirarin naka, dukda cewa hujja bata cikin muhimman abubuwanda kake la,akari da ita wajen yada labaranka. 

Kana kuma so da tsammanin kawai mu aminta da abunda kace ba tareda munyi bincike ba, kawai mu yarda da abinda kace don kaika fada. 

Abun banhaushi shine a naka ququmin tunanin duk wani wanda bai yarda da zuke ta mallenda kake yadawa ba makiyin yahudawa ne kuma makiyin  kasar Israila. 

Wannan irin soki burutsun ba a ganinshi a tattaunawa tsakanin masu ilimi da suka san me sukeyi amma shashasu irinku baku damu da sauya dokar tattaunawa ba ku kuma janyo dokar kasa zuwa daidai fahintarku. 
Gaskiya shine ramenda ka nuna kake cewa wai ramene daya bulla zuwa yankin mayakan Hamas ba mamaki ramene dake zubarda ruwa da sharar asibitin. 

Kana tsammanin ko ince kana umurtarmu da kawai mu aminta da duk wani abunda ka fada cewa wai wannan ramen ya bulla ne zuwa sansanin mayakan Hamas kawai don kace kowai don rundunar sojan Israila ta fadi haka?

Duk da haka shin wannan itace iya hujjarda zaku bayar ta kisan kiyashin mutane dubu goma sha biyu 12,000 fararen hula, wudanda daga cikinsu 6,000 yara ne kanana a zirin Gaza, sannan kuma kisan gillar mutane 186 a Yammacin Kogin jodan wudanda a cikinsu 46 yara ne kanana a cikin sati 5? Shin wannan itace iya hujjarku?

Wannan itace hujjarku ta kashe akalla yaro daya a zirin Gaza a cikin kowanne minti 10?

Wannan itace hujjarku ta mayarda Asibitin Alshifa makabarta, dake warin jini da tsutsotsin mutanenda kuka hana a bawa magani?

Wannan itace hujjarku ta jefa bamabamai a asibitoci da kashe kananan yara a injinan kyankyasa ta hanyar hana masu iskan oxygen da suke shaqa? Shin wace kalmace ta dace da irin wannan ta,addanci?

Shin wannan itace hujjarku ta kashe rabin mutanen zirin Gaza tareda rushe kashi 60% na gidajen zamansu da wasu gine gine masu muhimmanci a rayuwar dan Adam?

Kamar yadda Farfesa Norman Finkelstein Bayahude wanda ake girmamawa a fadin duniya ya buga a shafinsa na manhajar X,

" Yanzu awa 24 kenan da Israila ta mamaye asibitin Alshifa. Babu wasu alamun mayakan Hamas, babu alaman wajen ajiye makamai, babu wani wajen gabatarda yaki ko wasu hanyoyin sirri babu komai face gawarwakin yara kanana a injinan kyankyasa da aka daukewa wutar lantarki ".

Shin kai Ben Shapiro ko kuma abokanka Zayonawa ( Zionists) kuna inkarin wannan zancen ne?

Ko shakka babu kana matukar sani kyankyami, kai bawai kawai maridi, mahaukaci bane mai yunwar zubarda jini, kai wani irin mahaukacine mai shaawa da kuma burin zubarda jinin dan Adam. 

A daidai lokacinda duniya ke jimamin irin wannan mummunan taaddanci kai kuma saika zauna a kujerarka ka dauko ledar guggurunka kanaci kana raha kana jin dadin ana zubarda jinin mata da kananan yara a kowane dare. 

Ka tabbata fitinanne, karamin mutum mai buri da muradin ganin ana zubarda jin larabawa musulmai da kirista da zimmar shafesu duka daga ban kasa. 

Kaine mafi muni a tsakanin Hamas, ISIS, Boko Haram, Daesh, Al-Shabab, Islamic Jihad, Hezbollah da Al Qaeda a chakude a waje guda. Saboda kai bawai kawai mai goyon bayan ta,addanci bane, ko dan ta,adda ko mutum mai shaawar ganin ana zubarda jini bane kawai wanda bai dauki rayuwar dan Adam da wani muhimmanci bane kawai a,a kai kaman Hitler na Nazi kana kokarin Halasta irin ta,asarda kukeyi, kana yunkurin kuma saikasa kowa ya goyi bayan irin wanna ta,asa da kisan kiyashi da kuke. Ina mai tabbatar maka da babu wani mutum mai hankali kuma mai basira koda tamkar kwarar zarra da zai aminta da wannan matsayin naku. 

Irin kalaman batanci dana neman tada husuma da kakeyi a kan addinan musulunci da kiristanci shekaru wa shekaru da irin zagi da cin mutuncin manzon Allah Sallalahu alaihim   wa sallam da Isa Almasihu, ubangiji, na tun da can, kuma mahaliccin sammai da kassai, El shaddai, Elohim, Aadonai na farko da na karshe, dakake, ba abu bane da za,a aminta dashi tabbas irin mu,ujiza da kuma karama da sadaukarwa Yesu Almasihu ba abubane da za,a manta dashi ko ya shude ba tare da kula dashi ba. 

Tabbas kanada yanci da kuma damar riko da ra,ayinka da ace ko wane bayahude nada irin mummunan halinka na wariyar launin fata da kin jinin addinai mafi girma guda biyu a duniya, da duniyar nan ta cika da kin jiunin yahudawa, da duniya ta dauki Hitler a matsayin Sadauki, abun yabo kuma jagora na gari, amma saidai mun daukeshi a matsayin daya daga cikin mugaye, azzalumai da kuma macutan shuwagabanni a tarihin duniya. 

Ka zamo murya mafi kara a cikin muguwar tafiyar zayoniya, mafi iya yaudara, karya, cin mutunci da kuma rashin amana da adalci. Sannan ka sake jawowa kasar Israila karin bakin jini da makiya a duniya, ta hanyar yunkurinda kake na boye gaskiya, yada labaran karya da kuma goyon bayan mulkin mallaka a bayan kasa. 

Ba wai yarda da duk wani abuba da mutane kamarsu Dominique De Villepin, Professor Naom Chomsky, Jackson Hinkle, Mehdi Hassan, Clare Daley MRP, William Scott Ritter Jnr, Colonel Douglas MacGregor, Andrew Tate, Professor John Mearsheimer, James Corbyn MP, Julius Malena MP, Rashida Tlaib, Ilham Oman, Professor Cornel West, the Torah Jews, Professor Isa Pantami, Antonio Gutterres, Dr. Tedros Adhamon Ghebreyesus da sauran masu kiran a tsagaita wuta ba , masu goyon bayan zaman lafiya. Amma kowanne daya daga cikinsu ya nuna matukar tunani, da hujjoji akan gaskiya da adalci da kuma sanin hakkin dan Adam, tabbas sun kuma nuna iya fahimtarsu ta tarihi tareda irin tashin hankalinda ke faruwa a gabas ta tsakiya, musammam a zirin Gaza.

Sabanin kai, basu dimauceba da dimuwar rame, basu kuma makance ba, sannan kuma sonkai, da rashin kin gaskiya bai makantarda su ba. 

Kwanakin nan Prime Minister na kasar Canada Justin  Trudeau, wanda da dadewa ya kasa yin Allah wadai da kisan gillarda Israila ke yiwa Falasdinawa, saigashi kwatsam ya samu kwarin guiwar shiga sahun mutane maza da mata masu daraja akan yin haka, kwanaki kadan da suka wuce Mr. Trudeau a wata hira ta musamman da manema labarai yana cewa,

" Ina kira ga gwamnatin israila da ta kama kanta matuka, musani duniya na kallo a kafafen talabijin da kafofin sada zumunta, muna kuma jin jawabai daga bakin likitoci, da yan uwa da suka rasa iyayensu. Duniya na kallon kisan mata, kananan yara da jinjirai, dole ne a tsayarda wannan".

Muna fatan zai samu kwarin guiwar kira  da a tsayarda yakin gaba daya.

Sabanin kai Mr. Shapiro kowanne daga cikin wudannan mutanen, maza da mata yayi amfani da hankali, hujjoji da sanin ya kamata wajen cimma wannan matsayar. 

Amma kai bakada irin wudannan halayen na mutunci da sanin ya kamata. 

Bakada banbanci da wawan sarki, ko dan kama, dake tika rawa timbur a kasuwa da zimmar mutane su lura ko su kula dashi. Ko kuma sakaran dan dandi ko kuma tsohuwar yar barikinda barikin ta riga ta kare mata, wannan shine misalinka Mr. Shapiro. 

Ka kasance wani batacce, kuma tababbe, wanda babu sauran wata kafa da  zata tsamoka daga kanginda ka shiga ta hanyar makalewa a yanar yan anshin shatar Israila dake biyanka kudi domin ka kirkiro ka kuma yada labaran karya daga kasashen Amurka da Israila. 

Da zimmar kare muradun Israila ta kowane hali, idan wannan shine muradinka ba tareda kula da yancin dan Adam ba ko kuma wani digo na imani. 

Wannan shine muradinka, shine abunda ka aikata, kuma itace manufarka, baka damuba, saboda ka riga ka sayarda rayuwarka ga shedan shekaru da dama da suka wuce wajen neman suna da daudar duniya. 

Tabbas wutar jahannama  na jiranka Mr.  Ben, idan kaje can zaka iya ganawa Ku kumayi musayar basira tsakaninka da yan uwanka azzalumai kamarsu Hitler, Stalin, Pol Pot, Sarki Leopold na Belgium, Ghenghis Khan, Mohammed Al Baghadadi, Idi Amin, Jeanne Bedie Bokassa, Christopher Columbus, King Hero's, Pharaoh, Osama Bin Laden, Saddam Hussein, Nebuchadnezzar, Vlad mai tsirewa da sauran su. 

Zaka fahimci irin matsanancin halinda ka saka kanka ta hanyar goyon bayan da kabawa kisan kiyashin da kasar Israila ke a kasar Falasdinu  dama duniya bakidaya.

Na dade ina matukar kaunar kasar Israila, kuma har yanzu wani sashe nawa na kaunarta kamar yadda milyoyin mutane ka kaunarta a sassa dabban dabban na duniya, nayi kuka na kumayi bakin cikin harinda kungiyar Hamas takaiwa kasar a ranar 7 ga watan oktoba, bawai kawai nayi Allah wadai da wannan harinba namayi kira akan ya kamata a kawarda kungiyar Hamas daga doron kasa. 

Duk da haka zuciyata da tunanina da hankalina bazasu iya daukar irin ta,addanci da kisan kiyashinda Kasar Israila ke yiwa fararen hula ba a wannan lokacin. 

Yiman uzuri domin  inyi tsokaci tare kuma yin sharhi.  

Shin kamata yayi muci gaba da goyon bayan Israila duk da cewa tana aikata laifukan yaki, kisan kiyashi da ramuwar gayya ?

Shin kamata yayi mu goyi bayan kasar Amurka, muce ai Israila nada damar aikata kowane irin laifi na yaki, ta kuma sha batare da wani hukunci ba?

Shin kamata yayi mu tabawa ministan al,adu na kasar Israela dayace " bai kamata abar duk wani wanda ya daga tutar Falasdinu ya rayuba? Ko kuma a yayinda yace ya kamata a bugawa kasar Falasdinu bam din nukiliya? Ko kuma mu goyi bayanshi, lokacinda yace, "yakamata a tura yan kasar Falasdinu dake zirin Gaza mutum 2.5 milyan zuwa Sahara, ko a rabasu a matsayin yan gudun hijira zuwa kasashen duniya guda 100", wato akai mutane 25,000 zuwa kowace kasa?

Shin irin wudannan kalaman ne ya kamata mu fito mu kare mu kuma goyi baya?

Wudannan sune irin kalaman da dan ta,adda Ben Shapiro ke tsammanin mu fito mu runguma?

Shin ana tsammanin mu yi tsalle, cike da murna da annashuwa, lokacinda ministan tsaro na kasar Israila yace " koda masu raba alawa ne a zirin Gaza, kamata yayi a kawar dasu daga bayan kasa "?

Shin kamata yayi mu goyi baya lokacinda ministan tsaro na kasar Israila yace " Zamu iyayin abunda mukayi a Gaza a birnin Beirut "?

Shin irin wannan rashin imanin, kisan kiyashin da rashin sanin mutuncin dan Adam ne abun alfahari a yanzu? Shin kamata yayi muyi murna da hakan?

Shin babu sauran hankali da tunani a duniya ne?

Shin kamata yayi muyi amanna a lokacinda ministan kudi na kasar Israila yace " Babu wani abu mai kama da kasar Falasdinu, babu wani abu mai kama da tarihin Falasdinu, babu wani abu kamar yaren Falasdinu "?

Shin kamata yayi mu ringa tsalle, muna tafi, a lokacinda aka tambayi dan majalisar Israila cewa shin daidai ana kashe mutanenda basuji basu gani ba, mafiyawanci mata da kananan yara a zirin Gaza, sai yace " babu wani bafalasdine da baiji ba bai gani ba " kenan yana nufin Israila nada niyyar kashe kowane bafalasdine, mata da maza, yara da tsofaffi, kenan nufinshi a kawar dasu daga ban kasa?

Shin wai daga ina irin wannan rashin imanin ke fitowa ne? Kuma shin daidai ne muyi shiru mu kasa kalubalantar hakan?

Shin mu matsorata ne marasa zuciya? Shin saimu bari tsoro da son duniya ya hanamu fitowa mu fadi irin mummunan halinda zayoniyawa suka saka kasar Israila a ciki?

Shin littafin Attaura wato Bible bai gaya man cewa ba " Allah bai bamu ruhi na tsoro ba, saidai ruhi na so da kauna da kuma jarumta"?

Shin littafi mai tsarki bai mana gargadi akan, jin tsoron wanda zai iya kashewa ba, amma muji tsoron wanda zai iya saka mutum a wutar jahannama dungurun gum?

A yau Yahudawa sun hana sauran mutane cewa " daga rafi zuwa teku, Falasdinu zata samu inci" suna ikirarin cewa wudannan kalaman ba komai bane face kalaman manufar kare dangi, kuma suna ikirarin cewa wudannan kalaman ana yinsu ne da zimmar shafe kasar Israila daga bayan kasa, amma kuma su da Kansu sunada yancin cewa a shafe Falasdinu daga ban kasa. 

Su da Kansu suna shafe yara jinjirai na musulmai da kiristoci a zirin Gaza, sannan idan akayi la,akari da abunda ministan tsaro na kasar Israila yace wannan abun na gab da aukuwa a birnin Beirut na kasar Lebanon. 

Shin akwai wani zance na hankali a cikin irin wannan kin gaskiyar? Shin wannan shine adalci? Shin wannan bazai dami duk wani mai hankaliba? Shin ya dace ace a duniyar yau har wani na zance shafe wata al,umma daga ban kasa?

Shin kasar Israila, Zayoniyawa da yahudawa sunfi karfin doka ne? Shin suna da wata dama da zasuyiwa sauran mutane abunda su basa son ayi masu?

Shin kasar Israila bata doramu ne a wata hanyar zubarda jini ba da asarar rayuka, inda babu wata dokar yaki ko ta kasa da kasa dake aiki?

Shin laifukan yaki akan mata da kananan yara yanzu sun zama Halal a duniya ne?

Wannan zai iya zama haka amma a tunanin irin shirmamun mutane kamar Ben Shapiro, amma ba a duniya irin tawa ba. 

Yau a zirin Gaza ne hakan ke faruwa, gobe zai iya zama a garinku, kayi tunani a lokacinda kuke kallon borin kunyarda ke faruwa a kafafen yada labarai kamar CNN, aljazeera, BBC daga dakunanku. Hakan zai iya faruwa daku. 

Allah ya tsaremu yayi mana maganin masifa. Ku sake yiman uzuri in kammala wannan sashen da wudannan kalaman.

Na rubuta dubban kalmomi cikin sati biyu zuwa uku da suka wuce akan irin rashin hankali da rashin tausayi akan harinda kungiyar Hamas ta kaiwa kasar Israila a 7 ga watan Oktoba.

Babu wani dalilin kai wannan harin a daidai lokacinda aka kaishi, sannan wannan harin ya janyo mummunan ta,asa da tabarbarewa al,amurra. 

Tabbas wannan shine hari mafi muni da aka taba kaiwa kasar Israila tun lokacin mulkin Hitler, kuma nabi sahun milyoyin jama,a, daga fadin duniya wajen yin Allah wadai da wannan harin, na kuma nanata cewa kasar Israila nada yancin kare kanta da kuma kawarda kungiyar Hamas daga ban kasa.

Wudannan duk sun fada ne, a karkashin abunda lauyoyi ke kira dokarda aka samo akan yarjejeniya wato " settled law" a Hausance. Amma abunda ke bani mamaki shine duk lokacinda wasu daga cikinmu, muka nuna rashin jin dadinmu da kuma razana da kyamar irin wannan kisan kiyashin da kisan gilla da kasar Israila keyi a kasar Falasdin da sunan yakar kungiyar Hamas, ko kuma saboda mun nuna bacin ranmu dangane da ganin irin wannan mummuna sakamako akan mata da kananan yaran Falasdinu, da yadda ake nuno Asibiti ba magani, ga dubban majinyata kwance a kasa, ko kuma muka soki lamirin yadda Israila ke kai hari a kan asibitoci, makarantu, motocin bada dauki na gaggawa, coci coci da masallatai sai kaji yan anshin shatan zayoniyawa da Israila na zarginmu da laifin kin jinin Yahudawa da kasar Israila. 

Shin wannan ba shirme bane?

Shin bai kamata ace an nuna rashin amincewa da kisan kananan yara da mata musulmai da kirista ba kamar yadda ake nuna rashin goyon bayan kisan Yahudawa ba?

Shin dukansu ba yara bane kafin su kasance musulmai, kiristoci ko Yahudu?

Shin su yaran kirista da musulmai shin basuda yancin su rayu ne ko kuma basuda yancin a kare rayuwarsu da lafiyarsu a lokacin yaki kamar yadda yayan Israilawa keda wannan yancin?

Shin littafi mai tsarki ( Bible) ya gaya mana cewa kisan yara kanana koda na wane addini ne daidai ne?

Shin sabon alkawali na littafi mai tsarki bai haramta mana amfani da karfin makami ba, kisan kiyashi, kisan gilla, wariyar launin fata, rashin adalci, cuta, kisan kai akan kowanne dalili baza,a sake aminta dasu ba a karkashin sabon alkawali kuma aka hore mu da rikon amana, bin gaskiya, so da kaunar juna da kuma yafiya?

Shin littafi mai tsarki bai gaya mana cewa ba " karku bawa yara wahala, kuma muyi alaka da yara, mata, talaka, mara lafiya da nakasassu da adalci ba?

Shin ba saboda wannan dalilin bane ubangijin mu Yesu ya sauko ya sadaukarda rayuwarsa aka giciyeshi?

Shin baice muhimmin sanin darajar dan Adam shine mu yiwa mutane abunda mukeson suyi mana ba? Kuma muyi niyyar sadaukarda rayuwarmu akan ceton wasu ba?

Shin bai gaya mana cewa ba " nine mai ramuwa, zanyi sakayya" sannan kuma yace " idan aka mareka ka bada dayan kumatu" ba sabanin ramuwar gayya?

Wudanda suka kauda kai ga wudannan dokokin, suka ki yin amanna dasu, sannan suke cike da haushi, kunci da bacin rai tabbas sun zamo batattu kuma tababbi. 

Sun manta da  cewa sabon alkawali bawai kawai cikamakin tsohon alkawali bane, amma kuma an saukardashine domin ya rage radadi da tsananin tsohon alkawali, duk wanda bai yadda da hakan ba tabbas yana karatun wani littafin dabban ne ba Bible dina ba. 

Kiristocinda ke cewa Yahudawa da kasar Israila basa laifi, saboda su zababbun Allah ne, don haka zasu iya yin kisan kiyashi, su kashe mata da kananan yara, tabbas wannan kiristan ya tabe kuma yana da zunubin goyon bayan kisan kai da aikata barna a bayan kasa. 

Wannan mutumen ba asalin kirista bane, bashi da banbanci da bataccen bakin arne. 

Kiristanci bazai taba goyon bayan rashin adalci ba, da kuma kisan kananan yara musulmai. 

Me zaisa yahudawa suyi tunanin cewa zasu iya yin hakan kuma su tsira, batare da wani hukunci ya shafesu ba? Shin sunfi karfin kuskure ne, ko sunfi karfin doka ne?

Shin yahudawa na iya rike muguwar kiyayya akan musulmi ko kirista kawai saboda mutanensu sunsha azabar bautarwa? Duba da cewa milyoyin mabiya wudannan addinan, sun goyi bayansu, tareda taimaka masu a lokacinda suke cikin halin kuncin?

Shin wannan shine sulhun kasashe guda biyu ( two state solution)?

Shin ba saboda hakan bane akayi yarjejeniya " king David da kuma ta Oslo ba"?

Shin wannan hujjace ta nuna cewa duk musulmi dan Isis ne da Hamas amma ba duk Kirista bane dan Nazi?

Shin anya milyoyin musulmai da kiristoci basu sadaukarda rayukansu ba a yakin duniya na biyu inda suka yaki kasashen Jamus, Italiya, Japan, a karkashin tutar Nazi, domin su hana wudannan kasashen shafe Yahudawa daga bayan kasa.

Shin al,ummar duniya basu biya hakkinsu ba, da suka kafa sabuwar kasar Yahudawa, wato Israila a shekarar 1948 ta hanyar korar milyoyin Falasdinawa daga gidajesu ?

Wudannan tambayoyine masu matukar muhimmanci, duba da abunda israila ke aikatawa a Gaza, da kuma la,akari da cewa wasu daga cikinmu da sukace Israila ta wuce gona da iri, muka nemi cewa a tsagaita wuta sai mutane irinsu Ben Shapiro suka kakaba mana cewa waimu makiyan yahudawa ne, harda ma shugaban kasar Israila Benjamin Netanyahu a irin wannan zargi maras tushe. 

Shin dole sai an sanya duk sauran mutanen duniya sun aminta da irin kisan gillan da Israila kewa jinjirayen Falasdinu, amma kuma a hannu daya ayi Allah wadarai da hakan idan aka yiwa yayan Yahudawa?

Shin haka daidaine, kuma ya kamata?

Bana tunanin hakan.

Babu shakka duka rayuwa da kuma yara kanana nada matukar muhimmanci kuma yin kisan kiyashi ga kowanne jinsi na dan Adam abun ayi Allah wadai dashi ne. 

Tabbas duk Wanda ke tunani akasin haka kamar su Ben Shapiro to mahaukacine kuma dole ne a dakile irin wudannan tunanin da kalaman, idan kuwa ba haka ba zasu jefa duniya zuwa yaki duniya na uku. 

Shin a tunaninsu har iya wane lokacine al,ummar musulmi zasu iya jure ganin irin kisan gillanda akewa mabiya addininsu ?

Shin basu san cewa ba, duk lokacinda tura takai bango, har Wadanda ake turawa suka kai makula, to idan sukayi bore, za,a iya shiga wani mummunan yanayinda zai iya zama barazana ga kasancewar ita kasar ta Israila da kanta?

Shin mutane irinsu Ben Shapiro da yan uwansa Zayonawa basa tsinkayo hakan?

Shin kasar Israila na ganin da taimakon Amurka kadai zata iya yakar duka duniya? Shin ko ita kasar ta Amurka zata iyayin  wannan kasadar domin kare kasarda ta zamo barazana ga zaman lafiyar duniya?

Shin rayuwar musulmai da kiristoci kenan batada wani muhimmanci? shin akwai wani abunda jinin yahudawa yafi namu ne?

Shin akwai wani abunda jariran Yahudawa sukafi na larabawa, ko kuma namu?

Shin daga ina wannan rashin hankalin ke fitowa, sannan menene dalilinda yasa mutane da yawa ke kokarin kare wannan manufar?  Saboda dalilan siyasa ko kuma tsoron gungun karnukan farautar Yahudawa da Amurka?

Idan har za,a fadi gaskiya, irin wannan kin gaskiyar, bakin ganga, da zalunci, yana kan hanyar kai duniya cikin wani hali na kakanikayi da ba,a taba ji ko ganiba a tarihin duniya. 

Na fadi hakane saboda a halin yanzu duniyar musulmi na cike da bakin ciki da fushin abunda ke faruwa a zirin Gaza.

Babu wani abunda yayi nuni da hakan irin jawabin gwamnatin Taliban ta Afghanistan a lokacinda aka tambayesu dalilin kauracewa tattaunar kungiyar kasashen musulmai na duniya, da akayi a saudiya satinda ya gabata. 

Afghanistan ce kawai a cikin kasashen musulman da bata hallasci wannan taron ba.

Sun bayyana dalilinsu nakin zuwa taron kamar haka:

" Saudi Arabiya ta aikomana da takardar gayyata, amma shugabanmu ya mayarda ansa, cewa bama bukatar  takardar gayyata, Ku gayamana sansaninda sojojin musulmi zasu hallara".

Wannan itace ansa mafi tayarda hankali dana taba ji. 

Duk da cewa gwamnatin Saudiya ta janye takardar gayyatar amma wannan ansarda Gwamnatin Afghanistan ta bayar ya nuna irin fushi da bacin randa kasashen musulmi  ke ciki. 

Idan kuma zamu fadi gaskiya, wazaiga laifinsu?

Dole ne Israila ta yada takobi, ta daina irin kisan gillarda takeyi a Gaza da yammacin kogin Jordan, kafin su fusata gwamnatocin musulmi masu sassaucin ra,ayi, domin yin hakan ka iya tadoda wani sabon yunkuri na yakin Jihadinda zaiyi sanadiyyar mutuwar milyoyin mutane daga kowane bangare. 

Abun lurane bawai kawai kasashen musulmi ne ke cikin irin wannan bacin ranba, Afrika ta kudu da wasu kasashen na daban, sun yanke alakar diplomasiyya da kasar Israila, sun kumayi kira da a kama shugaban Israila Benjamin Netanyahu akan laifukan yaki, kisan kare dangi da kisan kiyashinda yakeyi a Gaza. 

Tabbas hannun agogo na kare matsewa Yahudawan Zayonawa dake alfahari da kisan kananan yara da jarirai. 

Duba da irin son zubarda jini, dagawa da kuma dakikanci, yasanya kasar Israila ta zamo wata barazana ta musamman ga zaman lafiyan duniya. 

Duniya nada zabin abunda ya dace suyi da kasar ta Israila amma a tawa fahimtar komai ya ta,allaka ne akan wudannan hikayoyin. 

Muyi dubi akan wannan : Idan zaki ya haukace, ya kuma yi kudurin kashe duk wani abu mai rai a jeji, saboda wasu tsirarun mayunwatan garken kuraye da suka kashe mashi yaya. Tabbas zaka fahimci irin fushinda zakin yake ciki, amma baza,a bar zakin ya kashe duk wani Abu mai rai a jejin ba akan wannan dalilin. 

Dole a kubutarda shi zakin daga hauka wucin gadi daya shafeshi ta hanya dirka masa harsashi aka, kafin ya kashe duk wani abu mai rai a jeji, Wanda ya kunshi harshi kanshi zakin. 

Wannan shine labaran kasar Israila, kuma idan ba,a garkameta ba to wannan itace makomarta. 

Wannan itace tsantsar gaskiya mai wahala, wacce wasu suka ki aminta da ita. 
Zanso ayiman uzuri in kammala wannan doguwar wasikar da wudannan kalaman. 

3 ga watan Oktoba, 2022 miladiyya Hilary Rodham Clinton tsohuwar babbar sakataren kasar Amurka, kuma yar takarar shugabancin kasar ta Amurka, ta yi rubutu kamar haka, a sashenta na yada zumunta a manhajar X.

" Idan har gwamnatin Rasha batason a zargeta da laifukan yaki to ta daina kai hare hare a asibitoci".

Ina mai kira ga Mrs. Clinton, matarda ta fito, bainar jama,a tana nuna farin cikinta akan kisan gillarda akayiwa marigayi Ghaddafi na Libya, data rage ciki, ta kuma rage munafunci, ta fito, tayi kira ga kasar Israila da shugaba Netanyahu, makamancin wanda tayi wa Rasha. 

Wannan zai taimaka matuka wajen sauya wannan mummunan lamari da hotonda rashin yin hakan ke nunawa duniya. 

Wani Bayahuden Amurka dan gwagwarmaya mai suna Miko Peled, yayi wani sharhi akan sojojin Israila, inda yake cewa " ta,addanci shine iya manufar sojin Israila ".

Duba da irin abunda ke faruwa a Gaza, yammacin kogin Jordan, da Lebanon, shin akwai wani mai inkarin wannan zancen? Shin wannan ba tsage gaskiya bane duk dacinta?

Shin abubuwanda ke faruwa a Gaza basuyi nuni karara ba tareda zama hujjarda ke goyon bayan kalaman Peled?

Sannan idanma wani na ganin Mr. Peled a matsayin wani shashashan da baisan ciwon kanshi ba, ko kuma baya kishin kasarsa ta Israila, to ya kamata mutum yayi la,akari da tarinsa da kuma asalinsa. 

Kakanshi Abraham Katsnelson, shine yasanya hannu a takardar samun yanci na kasar Israila. 

Babanshi Mattiyahu Peled yayi yaki a shekarun 1948 da 1967, amma daga baya yayi Allah wadai da yadda kasar ta Israila ta kwace yammacin kogin Jordan, Gaza, da yankin Sinai dake kasar Masar dama tudun Golan. 

Don haka wannan zuria ce wacce ta banbanta kanta kuma mai cike da dinbin tarihi da kyawon hali. Sannan kuma suna cike da tarihin sadaukarda rayuwarsu akan kasar Israila, tare kuma da kwarin guiwar gayawa shuwagabanninta gaskiya idan suka tafka kuskure. 

Peled shine yafi dacewa da a bawa kalamansa muhimmanci, fiye da dan anshin shatar gwamnatin Israila, dan maula wanda ba wani asalin kirki ne dashi ba wato Ben Shapiro. 

A nashi bangaren, Major Scott Ritter tsohon sojan kasar Amurka mai ritaya ya bada shawara mai matukar muhimmanci kamar yadda ya rubuta a sashenshi na sada zumunta a manhajar X:

" Dole ne Amurka ta kawo karshen wannan yaki, ta kawo tsagaita wuta mai dorewa, tareda aikawa da dakarun kasar Turkiyya, domin su bawa Falasdinawa kariya daga zakuncin Israila." Ya kara da cewa Sam Israila ko a jikinta, ta zamo kasa dake matukar muradi da jin yunwar zubarda jini.

Ritter ya buga kusa a tsakar kai, saura muyi fatan Joe Biden da sauran abokansa Zayonawa su saurari wannan kira da kunnen basira. 

Daga karshe shugaba Erdogan na kasar Turkiyya ya mika wannan gargadi ga kasar Zayonawa ta Israila inda yace,

" zanso inyi magana karara, kasar Israila kasar yan ta,addace. Suna kiran Hamas a matsayin yan ta,adda amma gaskiyar zance shine, Hamas jamiyyar siyasace, data ci zabe a falasdin.  Sannan bayanda sukaci zaben, sai kuka shigo kuka kwace masu yanci da mutuncinsu. Kashi biyu cikin ukun na mutane 12,000 da aka kashe a Gaza mata ne da kananan yara. Yace Israila na kai mummunan hari akan mata da kananan yara. Israila na cika bakin cewa zatayi amfani da makamin kare dangi na Nuclear ta kashe kowa da kowa a zirin Gaza. Don haka inason in tambayi Netanyahu: shin kanada makaman Nuclear ko babu? Ka gayaman idan har kanada zuciyar yin hakan. Kanata wani babatu kana alfahari, bazaiyi wani banbanciba ko kanada nuclear ko bakada, karyarka ta riga ta kare. ". 

Wannan ya nuna cewa yunkurin kararda Falasdin ba abu bane mai yiyuwa ba tareda mummunan zubarda jini ba. 

Saidai muyi fatan cewa Ben Shapiro da sauran yan anshin shatanshi Zayonawa wudanda ke muradin kawarda Falasdinawa daga ban kasa na saurare. 

Akace koba magana a zura ido ta ishi mai hankali. 

Abun takaicin shine duk da irin wudannan alamomin, shugaban Israila Benjamin Netanyahu ya kasa boye muradinsa da kishin zubarda jinin da ke damunshi. 

Ya tabbatarda hakan sati biyu da suka gabata inda yace "kasar Israila na yakine da Amalek".

Tabbas wadannan kalamai masu ban tsoro sunyi tasiri a zukatan masu saurare. 

Wudanda basu gane me yake nufiba, ina mai basu shawara, dasu karanta littafi mai tsarki, wato Bible tsohon alkawali, su gaya mana abunda Allah ya gayawa Yahudawa ta hanyar umurtarsu dasu yi kisan kare dangi wa duk wani namiji, mace , yaro ko babba dan kabilar Amalek a yunkurinsu na shiga da kuma mamaye kasa mai tsarki tare da kuma kafa kasar Israila. 

Tsatson Amalek a Bible ana kiransu da Amalekawa yau kuma sune ake kira da Falasdinawa. 

Shin kun gane abunda ake nufi?

Shin ko muna bukatar Karin hujjoji domin gane me Israila keda niyar aikatawa?

Shin akwai bukatar in sake cewa wani abu?

Allah muna rokonka da ka kare al,ummar Gaza, Falasdinawa, Gabas ta tsakiya da ilahirin duniya daga sharrin Yahudawa da duk wani mai  burin zubarda jini.  Koda yan ta,adda ne kamar Hamas ko Isis ko Islamic Jihad, ko kuma masu muradin kashe mata da kananan yara kamar sojojin Israila, masu muguwar kiyayya, da akidar wariyar kaunin fata da zakunci ta Zayoniyanci. 


( Anzo Karshen)


(Chief Femi Fani Kayode Sadaukin Shinkafi kuma Wakilin Dokan Potiskum lauya ne kuma tsohon ministan al,adu da yawon bude ido, sannan kuma tsohon Ministan sufurin jiragen sama a tarayyar Najeriya.)

Mohammed Bello Doka ya fassaara daga turanci zuwa Hausa. 

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post