Matakan Yakin Duniya na 3 Guda 14 na Femi Fani Kayode Sadaukin Shinkafi

A daidai lokacinda kungiyar Hamas takai mummunan hari a kasar Isralia  domin neman yanci na mulkin mallakan sama da shekaru 75 da kasar ta Israila ta shafe tanayiwa kasar Falasdin, tsohon ministan harkokin jiragen sama kuma tsohon daraktan harkokin na mussaman na aikin jarida a cibiyar yakin neman zaben shugaba Bola Ahmed Tinubu, Cif Femi Fani Kayode yayi wani hasashe akan abubuwanda ka iya kai su komo a sanadiyyar wannan harin. 

1. Kungiyar Hamas ta kaiwa kasar Israila harin bazata inda dubban mutane suka jikkata.

2. Kasar Israela ta kaddamarda yaki a zirin Gaza, ta kashe dubban yan ta,adda da wasu dubban fararen hula, mata da kananan yara. 

3. Kungiyoyin Hizbullah dana Islamic Jihad sun shigarwa Hamas tareda harba makamai masu linzame kasar Israila. 

4. Israila ta kaddamarda yaki da Hizbullah, takai farmaki a kasar Lebanon ta kuma mamaye wani bangare na kasar. 

5. Israila ta kaddamarda hari zuwa kasar Iran saboda bayarda makamai masu linzami kashi 70% da kuma kudade kashi 90% ga kungiyoyin Hamas da Hizbullah. 

6. Iran ta mayarda martani ta kuma kaddamarda yaki akan kasar Israila. 

7. Kasashen larabawa sun goyi bayan Iran sun kaddamarda yaki akan israila. 

8. Amerika,Ingila da kasashen turai sun goyi bayan Israila. 

9. Kasashen Rasha, Turkiya, Koriya ta Arewa, Afghanistan da sauran kasashen larabawa  sun goyi bayan Hizbullah da Falasdinawa sun kaddamarda yaki da kasar Israila da abokanta. 

10. Yakinda ake a kasar Ukraine ya kara cabewa inda kasar Rasha tayi was Ukraine kaca kaca ta kuma mallake ta. 

11. Kungiyar tsaro ta NATO ta kara kaimi a Ukraine, inda mummunan yaki ya barke a tarayyar turai. 

12. Kasshen China, Iran,Larabawa su shigarwa Rasha, kasashen Amerika, ingila dana tarayyar turai kuma su shigarwa Ukraine.

13. China takai hari ta mamaye Taiwan su kuma cika burinsu na mallakar tsibirin kudancin China. 

14. Amerika ta shiga cikin hargitsin kudancin China shikenan duk duniya ta shiga cakwakiya. 

Yan uwana abun bakin cikin a nan shine nan da yan shekaru kadan wannan badakalar na iya faruwa. 

Muna gab da shiga wani matsanancin hali na yakin duniya na uku, shin ko kunsan Da cewa wannan duk wata kulla, kulla ce da wasu masu burin kawo sabon tsari wa duniya suka kulla shekaru da dama ta suka shude?

Ina rokon Allah daya kare duniya daga sharrin kungiyoyin matsafa masu bautar shedan da Illuminati. 

Sharhi. 

A cikin wudannan matakan da Feni Fani Kayode ya tsara yakuma ja hankalin duniya kawo yanzu 4-5 sun tabbata. Muna rokon Allah daya kare duniya daga sharrin Shaidan da mabiyansa. Amin

Mohammed Bello Doka ya fassara.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post