Atattaunawa ta musamman da jaridar Abuja Network News tayi da Mai taimakawa shugan kasa na musamman akan Harkokin al,ummah Hon. Abdullahi Tanko Yakasai yana cewa shugaba Tinubu ya dauko hanyar magance matsalar tsaro data addabi yankin na Arewa maso Yamma.
Hakan ya biyo bayan wani rahoto da cibiyar daidaitawa da kuma magance matsalolinda suka shafi rikicin manoma da makiyaya Wanda shugaban kasa Tinubu ya kafa a karkashin tsohon Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Abdullahi Yakasai ya kara jaddadawa manema labarai cewa wannan tsarin da cibiyar ta kawo na sulhunta tsakanin manoma da makiyaya tabbas zai kawo maslaha ya kuma bada damar samun rage rikice rikicenda yankin ke fama dashi.
Yakasai ya kara da cewa mai girman shugaban jamiyya kuma tsohon Gwamnan Kano Dr. Ganduje mutum ne Wanda yasan asalin makasudin tashin hankali tsakanin manoma da makiyaya, don haka shawarwarinda ya kawo na samawa makiyaya wajen kiyo na zamani, tareda ababen more rayuwa tabbas zai kwantarda kayar baya ya kuma rage yawan tashin hankula.
Yakasai ya kara da cewa tsarin samarda injina da dabarun noma na zamani da cibiyar ke neman kawowa manoma tabbas da kuma wajajen kiyo na zamani da za,a yiwa makiyaya zai kawarda abunda ke kawo matsala a tsakanisu. Yana cewa " ai shiga gonakin manoma da makiyaya keyi suyi masu barna shine makasudin kawo tashin hankali a tsakaninsu, to idan har kowanne na wajensa na musamman bama zasu hadu ba ballantana a samu tashin hankali.
Akarkashin mulkin Tinubu, cibiyar a karkashin Dr. Ganduje ta kawo tsari kan zuba jari hadi da kayayyakin more rayuwa da kirkiro ayyukan yi, da koyar da sanao'i don inganta tattalin arzikin yankin. Da Samar da abinyi ga jama'ar karkara, ashugabancin Tinubu akwai yunkurin tanadi na masamman don karya lagon yan ta adda da masu kokarin tada kayar baya inji Abdullahi Yakasai.
Ya kara da cewa akokarinsa na samarda tsaro shugaban ya bada muhimmanci wurin ganin an samarda isasshin jami,an farin Kaya da kuma yunkurin sake aikewa da Karin Jami an tsaro a wurin da ake fama da rikice rikicen, da samuwar hadin Kai ga Jami an tsaron da kuma inganta ma,amala a tsakanin al,umma da gwamnati.
Ya kara da cewa Shugaba Tinubu yana da kudurin karfafa Jami an tsaro da kayayyakin yaki na zamani tare da turasu atisaye na musamman don yakar masu yunkurin tada kayar baya,don ganin an kare rayuka da dukiyoyin al,umma.
Yakasai ya kara da cewa gwamnati nada masaniya akan matsanancin hali rashin aikinyi, karancin ilimi da sauran matsaloli dake addabar yankin ya kuma kara da cewa tsare tsarenda cibiyar ta Dr. Ganduje ta shirya hanyoyin magance su.
Ni Fatima Hussaini dana Fassara
Muhammad Bello Doka ya rubuta
Haruna Musa ya tace nake cewa mu wuni lafiya
Tags
Hausa