Shin Tinubu na Son Arewa Kuwa?

Mohammed Bello Doka

Mahawarar datafi daukar hankulan yan Najeriya a kafafen sada zumunta dama dandula dabban dabban shine " shin shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu yanason yankin Arewa? 

Duba da irin gudumawarda yankin ya bayar wajen zaben shugaban kasa daya gabata wanda ya kawo shugan a karagar mulki dukda cewa ya fuskanci kalubale da dama. Amma sai gashi wajen bada mukamai a gwamnati wasu sassa dabban dabban musamman a yankin Arewa na ganin cewa kwalliya bata biya kudin sabulu ba. 

Kafin inje kan wannan tambaya, zanso inyi wata tambayar wacce da itace nake zimmar ansa tambayar shinko shugaba Tinubu na son Arewa ko bayaso. Tambayar kuma itace shin " Arewa na son kanta?" Ko ince shin Arewawa na son Arewa kuwa?"

Kafin muje da nisa zanso mai karatu yayi wani dan lissafi, ya tuna gwamnatin da ta gabata, wato a karkashin mulkin shugaba Muhammadu Buhari, a karkashin Buhari duk wani mukami mai amfani a kasar nan yana hannun yan Arewa, kamawa daga shuwagabannin tsaro da suka hada da sojoji, yan sanda, kwastam, gidan kaso, civil defence, DSS, NIA, harma da ministan tsaro, ministan shari'a, ministan kudi, ministan cikin gida da sauransu.

A wancan lokacin babu wani mukami mai muhimmanci daba a hannun yan Arewa yake ba, amma me Arewa ta amfana dashi a wancan gwamnatin? Idan mutum yace ba abunda Arewa ta amfana dashi baiyi kuskure ba, tunda koma wace irin moriya Arewar ta samu rashin tsaro ya sokeshi, ya sanya rashin aikin yi, karin talauci da jahilci sun addabi yankin. 

Arewa ta zamo cikin halin ni yasu, ga masifar 6arayin shanu da suka hana talaka sana,a, noma da kiwo, ga talauci da rashin aikinyi, sannan abun ban haushi mafi yawancin Gwamnonin na Arewa basa iya biyan mafi karancin albashi na dubu 30 a wata. 

A dayan bangaren kuwa su wudanda shugaba Buhari ya bawa amanar kare Arewar sunma fi sauran al,umma kuka, bayan sun noke sun cika aljihunansu da hakkin jama,a.

Karmu manta ministan jinkai ta wancan lokacin yar jahar Zamfara ce, Sadiya Umar Faruk amma duk wani tallafi na jinkai da rage radadin masifa da ake rabawa, jahar Legas tafi cin moriyarsa akan duka yankin Arewa, duba da wannan shin meye amfanin yan siyasar Arewa ga yankin na Arewa. 

Sannan karmu manta, a karkashin gwamnatin shugaba Buhari gwamnati tayi tsayin daka saida aka baiwa manoma tallafi da kuma bashi na noma, tsakani da Allah me manoman nan sukayi da wudannan makudan kudin? Da yawa basuyi noman ba, bayan haka suka raba kudin suka saka rabi a wasu kasuwancin, rabi kuma suka ringa sayen kayan noma a hannun manomanda mafi yawanci basu samu bashinba. Da suka sayi amfanin gonar me sukayi dashi? Boyewa suka ringa yi da zimmar ya kara tsada su sayar Wanda hakan yasa kayan abinci sukayi tashin gwauron zabi, karshe aka kara jefa talakan Arewa cikin matsala. Shin su wudannan yan Arewan suna son Arewa?

Sanna mu tuna shekarar 2020 a lokacinda gwamnati ta kakabawa yan kasa dokar hana fita, saboda masifar cutar Covid 19, wannan mataki yasa talakan Najeriya musamman na Arewacin Najeriya cikin wani matsanancin hali. A daidai wannan lokacin gwamnatin tarayya ta bawa jahohi taimakon kayan abinci domin rage radadin hana fita.

Idan bamu manta ba me gwamnonin Arewa sukayi, boye kayan abincinnan sukayi, me zasuyi dashi? Allah dai ya barwa kanshi sani amma daga karshe saida takai yan kasa sun fara bore suna fasa inda gwamnonin nan suka boye kayan abincinnan, abun takaici kusan duka sun lalace. Gwamnan da zai iya boye gero, dawa, masara, shinkafa da  aka bashi ya rabawa yan jaharsa saboda iftila,I shin wannan yanason Arewa?

Saboda haka maganar ko shugaba Tinubu nason yankin Arewa ko bayaso bai taso ba, babban alamar tambaya itace shin Arewa nason kanta ko batason kanta. Idan har talakan Arewa bai fahimci cewa yan Arewa sune babbar barazana ga Arewa ba tabbas yankin zaici gaba da fuskantar kalubalen talauci, rashin aikinyi da karancin ilimi. 

Muhammed Bello Doka shine mawallafin Abuja Network News, yana zaune a Abuja, Nigeria, aika sakon kai tsaye zuwa ga abujanewsmedia@gmail.com 


Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post