Kachalla HALILU SUBUBU Shugaban Ƴan Fashin Dajin Arewa Maso Yamma!


Yana Zaune Dajin Sububu Dake Yankin Galadi Ta Ƙaramar Hukumar Mulkin Shinkafi Jahar Zamfara. Duk Da Bayannun Baya Bayannan Akache Ya Karkata Hankalinshi Wajen Ginar Zinari a Yankin Ƙasar Bagega. Wanda Aka Tabbatar Da Chewa Mataimakinshi Mai Suna Kachalla Shehu Regeb Shine Ke Kula Da Yara Da Ɗinbin Tarin Makamanshi Dake Ƙarƙashin Ƙasa Ɓoye a Wani Wuri Mai Tsananin Sirri Ƙarƙashin Ƙasa. 

Ashekarar 2014 Wani Ɗan Jarida Sani Shaaibu Malufashi Ya Kai Ziyarar Gani Da Ido Wannan Daba Ta Halilu Dake Dajin Sububu. Inda Ya Tabbatar Da Halulu Sububu Shine Shugaban Ƴan Fashin Dajin Arewachin Wannan Ƙasa. Saboda Irin Tarin Dukiya Da Ɗinbin Makaman Da Yaga KACHALLA HALULI SUBUBU Ya Mallaka.

Akewayen Dajin Sububu Akwai Dabobin Ƴan Bindigar Ƴan Daborawa Da Ƴan Bindigar Gefen Maradun, Dana Dajin Kuka Tara, Dajin Ɓula Har Zuwa Dajin Bayan Dutsin Gundumi Da Gefen Dajin Raɓa. Kuma Har Wannan Lokachi Waɗannan Dabobi Suna Chigaba Da Hada Hadar Garkuwa Da Mutane Domin Amsar Kuɗin Fansa.

Dabar Ɗan Bindaga ALI ƊAN OGA Dake Dajin Kuka Tara, Tana Chikin Dabobin Dake Kusa Ga Wannan Daji Na Sububu. Inda Akeda Tabbacin Akwai Mutanen Gabaschin Sokoto Ana Garkuwa Dasu. Wanda Achanne Waɗannan Yaran Isa Su Biyu Akayi Garkuwa Dasu.

Akwai Tabbachin Awani Samame Da Aka Kai Masune Dajin Kuka Tara Ƴan Bindigar Suka Firgita Gabanin Akawo Dabar Tasu Suka Gudu Sukabar Waɗannan Yara Waɗanda Suna Ɗaurene Da Sarƙoƙi Bazasu Iya Guduba. Bayan Ƴan Bindigar Sun Dawo Dabarsune Suka Tarar Chewa Yaran Sunanan Ɗarme Basu Guduba Kuma Jami'an Tsaro Basu Kuɓutar Dasuba Domin Basu Shiga Dabarba Tunda Sunbi Yan Bindigar Lokachin Da Suka Razana. Nan Take Ƴan Bindigar Suka Kashesu. Subhanallah.

Muna Kira Ga Hukumomin Wannan Jaha Da Sucheto Alummar Dake Hannun Ƴan Bindiga Ake Garkuwa Dasu Dabobin Daban Daban Chikin Wannan Jaha. 

Ko Don Saboda Dalilin Jinƙan Bil'adama.......👌

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post