Gwamnan jahar Zamfara Dauda Lawal Dare yace yayi matukar kaduwa da samun labarin yadda yan ta,adda suka afkawa kauyen Sabon Gida kuma sukayi awon gaba da wasu bayin Allah.
Gwamnan ya fadi haka ne a sashen shi na Facebook, inda yake cewa, "Na yi matuƙar kaɗuwa da harin ta’addancin da 'yan bindiga suka kai a Ƙauyen Sabon Gida inda aka ɗauke wasu mazauna da ɗalibai."
A kan matakinda ya dauka kuwa Gwamnan ya kara da cewa "Ina samun labarin wannan ɓarna, na fara magana da jami'an tsaro, waɗanda suka samu nasarar ceto wasu cikin waɗanda aka ɗauka. Har yanzu kuma suna cikin daji wurin ganin sun ceto ragowar mutanen."
Sannan ya kara da yiwa mutanen Zamfara alkawalin cewa "Ba zan huta ba har sai na tabbatar da an tseratar da ragowar mutanen da ke hannun 'yan bindigan."
"Jami'an tsaronmu suna kan lamarin, da yardar Allah za mu yi nasara.'
Tags
Hausa