Abdullahi Yakasai (SSAP) Ya Ziyarci Ofishin Shugaban Jam,iyya Na Kasa Dr. Abdullahi Ganduje

Fassarawa: Fatima Hussain. 
 Babban maitamakawa shugaban kasa na musamman akan harkokin al,umma yankin arewa maso yamma,  wato Hon. Abdullahi Tanko Yakasai ya kaiwa shugaban jamiyyar APC ta kasa ziyarar bangirma da godiya a ofishinsa dake birnin tarayya Abuja a yammacin jiya Alhamis. 

Shugaban jamiyyar Dr. Ganduje ya tarbi bakin nasa cikin girmamawa da annashuwa ya kuma yabawa namijin kokarin Abdullahi Yakasai yakeyi wajen habbaka rayuwar al,umma da cigaban kasa. 

A nashi jawabin Yakasai ya yabawa shugaban jam iyyar bisa jajircewar shi da  cancantar shi akan shugabancin jamiyyar. Ya kumayi godiya da  goyon baya da shawarwarin da shugaban jammiyyar ke bawa matasa yan siyasa Inda yace wudannan shawarwarin ne suka kaishi ga cimma nasarar samun wannan matsayi.

 Ya kara taya shugaban jam iyya murna abisa lashe shariar da aka shafe makwanni anayi a kotu akan zaben gwannan kano, Inda Dr. Ganduje ya shafe shekaru takwas yana gwamana. Haka kuma Yakasai ya jaddada goyon bayan shi tareda alkawarin taimakawa shugaban Jam iyyar ta kowacce fuska domin cimma biyan bukata data shafi tsare tsaren jamiyya.  

 A martaninsa shugaban jam iyyar ya taya Abdullahi Yakasai murnar  samun wannan mukami na musamman, Inda yace wannan mukamin ya nuna irin jajircewa da kuma yarda da amana dake tsakanin Shugaban kasa da kuma Abdullahi Yakasai. Dr Ganduje ya Kara da cewar wannan Yana daga cikin alkawuran da shugaban kasar yayiwa matasa na aiki kafada da kafada tareda su domin gina Najeriya da kowa zaiyi alfahari da ita. 

 Ya Kara jaddadawa babban mai taimakawa  shugaban kasa shawara akan harkokin jamaa da cewar, wannan kujerar dama ce ta musammam  don yiwa al'ummamr Najeria aiki, cikin gaskiya da rikon Amana.

Dr. Ganduje ya kara da cewa a matsayinshi na uban jammiya a shirye yake ya taimakawa Abdullahi Yakasai wajen sauke wannan nauyi da Allah ya dora mashi. Ya kuma roki Allah daya taimakesu baki daya wajen gina kasa da yan Najeriya zasuyi alfahari da ita.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post