Hankali Da Gada Femi Fani Kayode Ya Ja Kunnen ECOWAS Akan Yakar Nijar


Fassara: Mohammed Bello Doka. 

Bayan kace kace da kuma chakwakiyarda zaben da kuma nadin ministocin da shugaba Tinubu ya qaddamar ya janyo, lokaci yayi da yakamata yan qasa mu natsu mu kuma mayarda hankali ga muhimmin lamarinda ke faruwa masu matsanancin hatsari. 

Dukda matsalolinda kasa ke fuskanta a bangaren tsaro dana tattalin arziki wani abu mafi tada hankali shine yanayinda ke faruwa a jam,huriyar Nijar. 

Ya kamata muyi la,akari da wasu mihamman abubuwa kamar. 

Kasashen Sudan, Chadi, Burkina Faso, Mali da Gini duk sun fuskanci wannan kalubale na juyin mulki a cikin shekaru 3 da suka gabata. 

Sun hada wata qugiya ta shuwagabanni sojiji da ya tashi daga kasar Gini a yammacin Afrika ta gamma ya yanka ya zagaya I zuwa kudancin Afrika ta yamma ta zirin Tabkin Chadi zuwa gabaccin Afrika da ya dangane da bahar maliya. 

Abun la,akari ne da kuma lura da cewa wannan kugiya ta shuwagabanni sojoji na kara zama barazana ga demokradiyya da yancin dan Adam a Afrika. Yana kuma kara zama barazana ga zaman lafiya da tattalin arziki ga nahiyarda ke fama da kuncin talauci. 

Tabbas ya kamata muyi himma da hanzari domin kare hakkin dan Adam da kuma mulkin demokradiyya a nahiyar Afrika. Tabbas hakan abune mai kyau amma bazamu cimma wannan manufarba ta hanyar amfani da sojojin haure ko kuma ta hanyar fatwa qasar Nijar da hari da zimmar tsaida demokradiyya. 

Dauwammarda demokradiyya zai yiyune idan masu mulki sunyi mulki kan adalci, kwantata gaskiya da kuma adalci. 

Tabbas wannan itace kawai hanyarda za,abi domin dauwammarda demokradiyya a Afrika dama duniya baki daya. 

Domin idan masu mulki na mulki na adalci tabbas duk wani soja dayace zai tashi yayi juyin mulki tabbas zai hadu da fushin dubun dubatar yan kasa da suka aminta ta adalcin gwamnatinda suka zaba.

Idan haka ta kasance ba wani shugaba da zai bukaci wasu sojoji su fito daga wata kasa su mayarda shi kan mulki a kasarsa. 

Wannan shine abunda shugaba Bazoum ya kasa fahimta. 

Ya bar mutanenshi suna fama da talauci sakamakon handama da babakeren gwamnatin faransa wadda ke cigaba da yiwa kasar mulkin kama karya a wani sabon salo na mulkin mallaka. 

Wannan shine dalilinda ya janyo juyin mulki a kasar Nijar. 

Ina fatan shuwagabannin Afrika zasu lura da wannan. 

A tawa fahimta Sam babu wata basira ko hikima a cewa wai kasashen ECOWAS su farma kasar Nijar da yaki domin dauwammarda demokradiyya. 

Abun mamaki shine bayanda dakarun sojojin ECOWAS din suka kammala zamanda sukayi a birnin Akra na kasar Gana, hafsoshin sojojin sun fitarda sanarwa cewa " A shirye suke su aukawa kasar Nijar."

Wannan ya sabawa shawarwarinda babban kungiyar tarayyar Afrika ta AU ta bayar da kuma nuna rashin aminta da kasashe kamarsu Aljeriya suka yi da yakar kasar ta Nijar. 

Wannan dalilin ne yasa na yanke shawarar in tambayi kasashen ECOWAS na yammacin Afrika tambayoyi kamar haka. 

Shin zamuyi nasara idan muka afkawa kasarda talakawan qasar ke matukar goyon bayan gwamnatinda muke so mu canza masu? Har suke tattaki da nuna goyon bayan ta?

Tabbas wannan zai janyo yan kasar su goyawa gwannatinsu baya idan mukayi wani yunkuri na yakarsu, hakan zai zamo wani dogon yaki Wanda babu tabbacin Nasara a cikinsa. 

Karmu manta kasar Rasha tayi tsammanin  zata ci karfin Ukraine  cikin sati biyu amma yau ana neman shekaru biyu kenan yakin bai kareba. 

Bayan haka tambaya ta gaba shin an riga an shirya  sojojin ECOWAS da zasu yaki kasar ta Nijar? Ko kuma za,a raba ne kowace kasa ta dauki nauyin yakar nata bangare sai a hadu a tsakiya?

Sannan ina ne hedikwatar wudannan sojiji zata kasance kuma soja nawa ko wace kasa zata bayar?

Tambaya mafi muhimmanci shin wace kasa zata dauki nauyin cike gurbin hadakar sojojin MNJTF dake yakar Boko Haram ta gefen tabkin Chadi domin babu shakka Nijar zata jqnye sojojinta. 

Sannan idan kasashen Burkina Faso da Mali suka hada kai kaman yadda sukace zasuyi shin wazai dauki nauyin yakar yan ta,addab Boko Haram, al,qaeeda da sauran yan ta,addarda ke wancan bangaren na iyakar kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar?

Shin da gaske sojojin hayar Wagna na Rasha dake kasar Mali sunshiga yarjejeniya da kasar Nijar domin su tayasu yakar kasashen ECOWAS? Idan hakan yq kasance shin mun shirya yadda zamu magance shigan mugayen makamai hannun fararen hula? Kuma mun shirya hanyarda zamu magance da kuma kula da masu safarar miyagun kwayoyi ? 

Sannan abu mafi muhimmaci shin wazai daukin nauyi kudadenda za,a kashe wajen wannan yaki? Shin majalisar dinkin duniya ce zata daukin nauyin kudaden ko Amurka ? Domin a yanzu Najeriya batada kudadenda zata iya daukar nauyin yakin nan kamar yadda mukayi a lokacin Ecomog a laberiya da sauransu. 

A tawa fahimtar ana bukatar aiki da hankali da kuma lisaafi. Amfani da diplomasiyya shine kawai mafita a wannan hali. Dole muyi amfani da basira wajen tunkarar wannan yanayi. 

Idan kasar Nijar ta bude kofarta yan ta,addan Isis, alqaida, Boko Haram da sauransu suka duraro Najeriya to duk jahohinda ke iyaka da Nijar daga sokoto zuwa Lagos zasu kasance cikin hatsari. 

Don haka a nawa gani idan kasashen Amurka da Faransa, Ingila da tarayyar turai sun damu ta daumarda demokradiyya, sun kuma damu da kare muradunsu a kasar Nijar to su zo da Kansu su yaki kasar Nijar su mayarda Bazoum amma wannan yakin banamu bane mu yan Afrika domin babu wani abunda zamu amfana dashi sai asara kai da kai. 

Femi Fani Kayode.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post