Zan Yiwa Kowa Adalci a Matsayin Shugaban Kasa- Tinubu.... Yayi wa shuwagabannin addinin musulunci na kudu maso yamma alkawalin habbaka tattalin arziki

A ci gaba da tattaunawarda yakeyi da shuwagabannin addinin musulunci dan takarar shugaban kasa a jamiyyar APC Sanata Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin farfado da tattalin arzikin kasa domin amfanar yan Najeriya.

A yayinda yake magana da shuwagabannin addinin musulunci na kudu maso yamma a wani taro na musamman a garin Ibadan babban birnin jahar Oyo dan takarar ya yaba namijin kokarin da malaman addinin keyi wajen tabbatarda zama lafiya a yankin nasu.

Tinubu yace wannan zaben mai zuwa zabene da tarihi bazai taba mantawa dashi ba saboda muhimmancinsa,  yayi kira ga shuwagabannin dasu kara kaimi wajen kira ga mabiyansu da su fito kwansu da kwarkwata domin su cika wannan muhimmin aiki na zabe ba tare da sun bada kai bori ya hau ba. Ya kuma shawarce su dasu guji fadawa tarkon makaryata masu neman haddasa rigima a kasa.

A cewarsa abunda ya kamata jama,a suyi la,akari dashi kafin zaben dan takara shin wane irin kokari yayi a can baya. Don haka ina shawartarku daku yi kira ga mabiyanku  suyi amfani da hikima da basira wajen zaben. 

Dan takarar mafi rinjaye a zaben da za,a gudanar a 2023 yayiwa yan Najeriya alkawalin cewa idan suka zabeshi zai kasance mai rike gaskiya da kuma yin adalci wanda yayi daidai da tsarin addininsa na musulunci. 

Shugaba wanda yake a kasa irin tamu mai addinai dabban dabban dole ya zamo mai adalci ga kowa kamar yadda kundin mulki ya tanada.

Ya kuma yi nuni da irin nasarorin da ya samu a lokacinda yake gwamnan jahar Lagos don haka yayi kokarin yin amfani da basirorinda ya samu wajen sabunta wa yan kasa zato.

A bangaren tsaro kuma Tinubu yayi alkawalin kawo karshe ta,addanci da sauran miyagun laifuka ta hanyar amfani da kimiya da kuma koyarda jami,an tsaron kasa.

Ya kuma yi alkawalin zai sauyawa tattalin arzikin kasa akala inda tsarin zai kawo wa Najeriya akalla 6% na ci gaba a fanni tattalin arziki. 

Ya kuma yi alkawalin mayarda hankali wajen habbaka wasu masana,antu da zasu ringa kawowa Najeriya kudin shiga domin rage dogaro da man fetur ko ma,adinai. 

Dole muyi hanzari mu sauya akalar tattalin arzikin kasa domin samarda ayukanda zasu tabbatarda wanzuwar arziki a kasa.

Dole mu habbaka kamfanoni masu kere kere domin su samarda ayuka ga yan kasa. Muna bukatar a kalla samun ci gaba na kashi shida cikin dari 6% a kowanne shekara. Muna kuma bukar habbaka kamfanoni, samarda kayan more rayuwa hanyoyi gadoji da ginegine haka ma dole a a tabbatarda samun wutar lantarki da kuma sauye sauye wajen a kasafin kudin kasa.

A bangaren noma kuwa yayi alkawalin samarda yalwa mai dorewa ta hanyar habbaka fasahar noma domin samarda abinci domin a tabbatarda babu wani yaro ko yarinya da zata kwanta da yunwa saboda rashin abinci.

Daga karshe ya roki Allah, kada muga ranarda wata uwa zata fuskanci matsinda zaisa ta lallaba yayanta suyi bacci da yunwa saboda rashin abinci. Ya kara da rokon Allah ya taimake wajen yalwata samun arzikinda zaisa ko wanne yaro ko yarinya su taso cikin samu da yalwa domin sabunta zato.

A nasa jawabin shugaban kungiyar malaman addinin musulunci na kudu maso yamma a lokacinda yake jawabin tarbar dan takarar  Alhaji Rasaki Olasejo yace an hada wannan taron ne domin dan takarar ya samu tattaunawa da shuwagabannin addinin musulunci na yankin domin ya gaya masu wane irin tsari yake dashi ga al,ummar Najeriya idan aka zabeshi a matsayin shugaban kasa.

Haka shugaban kungiyar Anwar-ur-Deen na kasa Sheikh Ahmad Abdulrahman yace taron ba fage bane ta kamfe ko kuma nuna goyon baya ga Tinubu.

Saidai an hada wannan taron ne domin su ji wane irin tsari dan takarar keda shi wajen kawo ci gaba ga Najeriya kamar yadda ya kawo a Birnin Lagos lokacinda yana gwamna. 

Tinubu yaje wajen taron tareda wasu shuwagabanni na yankin na kudu maso yamma kamarsu mataimakin gwamnan Lagos, Dr. Femi Hamzat, da dan takarar gwamnan jahar Oyo Senator Teslim Folarin, tsohon kakakin majalisar wakilai  Dimeji Bankole, mataimakiyar shugaban yakin neman zabensa Hadiza Bala Usman, Sai dan majalisa Fatai Buhari daga Oyo wanda dan majalisa a lokaci mai tsawo.

Kafin wannan taron dan takarar yayi hira ta musamman da shuwagabannin addinin kirista darikar Pentecostal na jahohi goma sha tara na arewacin Najeriya. Inda suka tattauna akan abubuwanda ya tattauna da shuwagabannin na musulmi.

Ya gayawa shuwagabannin na addinin kirista da cewa idan aka zabeshi a matsayin shugaban kasa zai tabbatarda gaskiya da adalci ga kowane dan Najeriya.

Offishin yada Labarai na Tinubu
Tunde Rahman
Disamba 11, 2022

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post