Tinubu Alkhairi Ne Ga Arewa Inji Ambassador Rashida Mai Sa,a.


Kyakkyawar Jarumar Kannywood kuma shugaban kungiyar mata yan film din Hausa Ambassador Rashida mai sa,a tace Senator Bola Ahmed Tinubu alkhairi ga al,ummar arewa dama Najeriya baki daya.

Ambassador Rashida wadda member ce ta babbar cibiyar yakin neman zabe reshen mata na jamiyyar ta APC , kuma jigon APC tace duk wani rade rade da farfaganda bazaisa yan Arewa su manta da alkhairin da Sanata Bola Ahmed Tinubu ya kawo wa arewa ba.

A cewar ta so uku kenan Tinubu yana goyon bayan yan arewa da zimmar su samu shugabancin kasar nan. Yayi wa Atiku Abubakar a jamiyyar AC, ya tsaida Ribadu a Jamiyyar ACN haka kuma ya tsaya tsayin daka ya goyawa Buhari baya ya samu tikitin jamiyyar APC Wanda Allah cikin ikonsa yasa Buhari ya samu ya lashe zaben, haba jama,a idan bamu goyi bayan Tinubu ba ai munyi butulci.
Tace a shirye take ita da magoya bayanta suci gaba da shiga gida gida, sako sako kai harma daki domin su tabbatar mata da maza tsofi da yara sun fito sun rattabawa Bola Tinubu ruwan kuri,u tace domin wannan shine kawai adalcinda zasu iyayi.

Bayan haka kuma Sanata Tinubu yana da kwarewa da sanin makamar aiki, yana da dattako, sanin ya kamata kuma yasan matsalolin Najeriya.

Tayi kira ga yan Najeriya musamman yan Arewa dasu hada karfi da karfe su zabi Sanata Bola Ahmed Tinubu domin ance yaba kyauta tukuici.

A kano kuma tace ai da sunan Allah Gawuna da Garo sun riga sunci zabe domin su a yanzu rantsarwa kawai suke jira. Domin tanada yakinin cewa kanawa bazasu sake reshe su kama ganye ba. Gwamna Ganduje yayi mun gani kuma tare da Gawuna da Garo aka yi duk wannan dawainiya don haka sune sukafi dacewa da su ci gaba da wannan aikin alkhairi.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post