Ta Taya Zaku Kare Kanku Daga Ciwon Koda (Kidney Disease)


1. A yawaita shan ruwa
2. A rage cin nama da yawa a lokaci ɗaya (in za'a ci sai a rarraba lokutan ko ranaku).
3. A rage shan abubuwa da suke kunshe da sinadarin Potassium mai yawa sosai (a yawaita karanta bayanai da suke jikin tambarin abubuwa (label).
4. A gujewa yawan shan magungunan kashe zafi, radadi, ciwo irin su Diclofenac, Aceclofenac, Ibuprofen, Ciwo takwas, ciwo ashirin 😂 da sauran su.
5. A yawaita duba yanayin jini, in mutum na da hawan jini, toh ya duba sau ɗaya a sati, in bai dashi, sau ɗaya a wata.
6. A kula da yanayin sugan dake cikin jinin mutum (Blood Sugar) Sannan a tabbatar da cewa magungunan da mutum ke amfani dasu likita ne ya rubuta su.
7. A gujewa shan maganin gargajiya, a gujewa maganin gargajiya kamar da an ganshi a ji kaman anga annoba.
8. In likita ya rubuta magani, a tabbatar da an samo shi a tabbataccen Pharmacy saboda akwai wajajen da suke siyar da magunguna na bogi.
9. A dinga girki da asalin man gyada (mai da aka matse gyada aka same shi), sannan a yawaita mu'amala da manja sosai.
10. In ana jin fitsari a daure a yi shi, matse fitsari ba gwaninta bane.
11. A magance duk wata rashin lafiya da aka san ta bayyana.

Sunana Pharmacist Musa A Bello, likitan magunguna, gudummawa na shi ne fadakar da jama'a, Kai kuma naka gudummawar kayi like da share wasu su amfana.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post