GUDAJE KAZAURE: SHUGABAN BABBAN BANKI NAJERIYA BARAZANA NE GA TATTALIN ARZIKIN KASA.


A wata hira ta mussamman da sakataren kwamitin cirewa da ajiyar kudi a asusun banki Hon. Gudaje Kazaure ya zargi shugaban babban bankin Najeriya CBN da cin amanar kasa, cin hanci da rashawa da kuma yunkurin karya tattalin arzikin arewacin Najeriya. 

Kazaure dai a cikin hirarda yayi da yan jarida ya yi bayani akan yadda shugaban babban  bankin na CBN ya boye sama da Naira tiriliyon 80 a wasu asusun ajiye kudi na banki guda uku inda ya sabawa dokar tattara kudaden gwamnatin a asusu bai daya. 

A cewarsa wannan kudi ne da babban bankin ke cirewa masu ajiyar kudi da hada hada dashi a banki. A duk lokacinda mutum ya tura kudi koya cire koya sayi wani abu to banki kan cire masa Naira dari wanda ake tattarawa a wani asusu na dabban sabanin asusu na bai daya kamar yadda doka ta tanada. 

Gudaje ya zarki shugaban babban bankin da boye wannan kudin ba tare da ya sanarda shugaban kasa ba inda ake amfani da wannan kudin wajen bawa kamfanoni bashi abun ban haushi Gudaje yace wannan kudin ne ma shi shugaban na babban banki ke amfani dashi ya bawa Najeriya bashi.

A takaice dai ana amfani da kudin Najeriya a bawa Najeriya bashi kuma ana tsammanin Najeriya ta biya bashin hadda kudin ruwa. Abun tambaya anan shine ya aka dauki dogon lokaci ana irin wannan tabargaza ba tare da sanin fadar shugaban kasa ba?

Wannan cin amanar kasa ne tare da barazana ga zaman lafiyar al,umman kasa. Gudaje yayi Allah wadai da wannan hali ya kuma sha alwashin sai yasa an cire shugaban babban bankin an kuma gurfanarda shi a gaban kuliya da shi da duk wani mai hannu a wannan mummunan aikin.

Gudaje ya kuma zargin shugaban na CBN wato Godwin Emefile da yin yunkurin karya tattalin arzikin kasa musamman kananan yan kasuwa daga yankin arewa wudanda basu cika ajiya a banki ba. Haka kuma yace dokarda ta hana mutum cire kudi sama da Naira dubu ashirin a rana zata talauta sama da mutum milyan goma sha takwas dake sana,ar POS     

Daga karshe Gudaje ya zargi alkalin alkalai na kasa dama ministan sharia da hada kai da Emefile wajen ganin an tsayarda wannan binciken da sukeyi. Amma Gudaje yasha alwashin babu Wanda ya isa ya tsayarda wannan binciken kuma sai an cire shugaban babban bankin daga mukaminsa domin a samu damar yin bincike na hakika.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post