FEMI FANI KAYODE YA HADAWA ATIKU ABUBAKAR JINI DA MAJINA


Tsugune dai bata karewa dan takarar shugaban kasa a Jam,iyyar PDP ba wato tsohon mataimakin shugaban kasar Nijeriya Atiku Abubukar. Atiku yayi wasu kalamai da suka ci gaba da janyo kace nace a kafofin yada labarai dama shafukan sada zumunta.

Tsohon mataimaki shugaban kasan dai ya sake shan alwashin sayarda babban kamfanin mai na kasa wato NNPC, da manyan tashoshin jiragen ruwa hadi da wasu manyan kadarorin gwamnatin tarayya, inda yace gwamnati bata bukatar wudannan kadarorin wai a tasa fadar gwamnati tafi bukatar kudade domin aiwatarda ayukkan yau da kullum.

Amma babban daraktan harkokin jarida na musamman da kuma kafofin sada zumunta, tsohon mai bawa shugaban kasa shawara kuma tsohon minister Femi Fani Kayode yayi fancakali da wannan zancen inda yayiwa Atiku raddi kamar haka.

" Kamar yadda ka sayarda gwamnoni biyar na jam,iyyarka a bakin kwata, ka sayarda rayuwarka wa shedan sannan kuma ka sayarda mutuncinka ga Dino.... " da dai sauran kalamai dake nuna cewa dan takarar na PDP na mu,amalar saduwa da maza yan uwansa.

Idan jama,a basu manta ba Femi Fani Kayode ya taba zargin dan takarar na PDP da wasu jigajigan kungiyar neman zabensa da luwadi, madigo da wasu halaye marasa dadinji inda kuma ya nemi su wudanda ya zarga din dasu fito su musunta ko kuma su kaishi kotu domin ya fito ya bada hujjoji, amma ji kake kamar an shuka dusa ba Wanda ya fito daga cikinsu domin yi masa inkari.

Banda Femi Fani Kayode haka masu ruwa da tsaki a kafafe mabanbanta sunyi Allah wadai da wannan zance na Atiku Abubakar duba da cewa Atiku ya jagoranci sayarda wasu manyan kadarorin gwamnati a lokacin yana mataimakin shugaban kasa kamarsu, kamfanin wutar lantarki na kasa NEPA, Kamfanin Wayar tarho da salula na kasa NITEL, kamfanin kera karafa na Ajakuta dama wasu kamfanoni da yawansu yakai sama da kamfanoni 500.

Babu wani kamfani da ayau za,ace yan Najeriya sunci moriyarsa cikin sama da kamfanoni 500 da Atiku Abubakar ya jagoranci sayarwa. Abun ban haushi duk wudannan kamfanonin Atiku ya sayarwa kansa ne, da kuma abokansa da yammatansa.

A wata hira da dan takarar shugaban kasar yayi a shekarun da suka gabata yataba ikirarin idan ya zama shugaban kasa zai azirta abokansa kamar yadda tarihi ya nuna Atiku ya saba azirta yan uwa da abokansa ko ace ya saba karawa mai karfi karfi ta hanyar sayar masu da masana,antun gwamnati a wulakance Wanda maimakin su gyara wudannan kamfanonin saisu kashesu ta hanyar sayarda duk wasu kayan aiki, injina da karafa, wayoyi dama komfutoci kamar yadda suka kashe kamfanin Nitel, Kamfanin jiragen kasa, kamfanin kera karafa da sauransu.

Bahaushe dai kance baki shike yanka wuya, inda yan Nijeriya a kafafe dabban dabban na sada zumunta suketa Allah wadai da wannan kudurin suna kuma kira ga yan Nijeriya da mu yiwa kanmu kiyamul laili.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post