DAGA CIKIN MATSALAR 'YAN DARIQU A CIKIN ADDININ MUSLUNCI!!! by Mallam Abdulkadir Sulaiman Shinkafi

Babbar matsalar 'yan dariqu acikin addinin muslunci anan ita ce: Zaka ji suna da'awar cewa su ne masoya Manzon Allah s.a.w. amma abu ne mai wuya ka samu cewa malaman su suna dauko littattafan Hadisan Annabi Muhammad s.a.w. suna koyar da al'umma, kamar Saheehul-Buhari, Saheehu Muslim, Sunanut-tirmithi, Sunanu-Abi-Dawud, Sunanubnu-Majah da dai sauran littattafan Hadisi da muke dasu! Amma a hakan su ne suke da'awar cewa suna son Annabi s.a.w.! 

To wai ku 'yan dariqu in har da gaske kuna son Annabin a da'awarku me yasa ba zaku watsa maganganunsa ba da ayyukansa ba don ayi koyi dashi?! Me yasa baku shahara da hakan ba?!

Me yasa kuke ihu idan aka ce ku kawo hujjah daga cikin Hadisan Annabi s.a.w. akan wasu ayyukan darikunku da kuke aikatawa?! Idan har da gaske ku masu bin koyarwar Annabi ne da gaske a da'awar ku?
 
Me yasa ba ma ji kuma ba ma ganin kuna koyar da al'umma littafan dariqunku a fili kamar su #Jawahirul_Ma'ani, #Alyaquutatul_Faridah, #Al_Ifaadatul_Ahmadiyyah, #Alfat_hurrabbani_Fii_ma_yahtaaju_Ilaihil_Muriidut_Tijani da dai sauran su, irin yadda malaman mu ahlussunnah wal jama'ah ke fitowa a fili suna koyar da al'umma littattafan Sunnar Annabi s.a.w.?

Me yasa kuke ihu kuna fada idan ana karantawa jama'a littafanku na dariqu?

Wannan yake nuna mana cewa abinda yake cikin littafanku ba tsintsar gaskiyar koyarwar Sunnar Annabi s.a.w. ba ce ko son sa! Bin son zuciyar shehunan ku ne kawai!

Ya ku 'yan dariqu ku dawo ku bi koyarwar Sunnar Annabi Muhammad s.a.w. a bisa fahimtar salafussaliheen (Magabata na kwarai) sai ku zauna lafiya.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post